ABNA: Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar da rahoton cewa, a jiya Lahadia aka sanar da sakamakon karshe na zaben shugaban kasar da aka gudanar a kasar Guyana tun a cikin watan Maris da ya gabata, inda aka sanar da sakamakon farko a cikin watan Yuni, wanda ko a lokacin Irfaan ne a gaba, a jiya kuma aka sanar da sakamakon karshe, wanda ya tabbatar da cewa dan takarar jam’iyyar adawa a kasar Mohammad Irfaan Ali ne ya lashe zaben.
Mohammad Irfaan Ali wanda musulmi ne kuma dan siyasa a kasar ta Guyana da ke kudancin Amurka, ya taba rike mukamin ministan gidaje a kasar, wanda kuam yake da karbuwa a wurin mutanen kasar.
Kasar Guyana wadda adadin mutanenta bai wuce 800,000 ba, tana cikin kasashen duniya masu fama da talauci, inda al’ummar kasar sun dogara ne kawai da noma.
Amma a cikin lokutan baya-bayan nan an gano cewa kasar tana da dinbin arzikin danyen man fetur kwace, wanda kuma nan ba da jimawa ba kasar za ta kasance a cikin kasashen duniya masu arzikin danyen man fetur da ke fitar da shi zuwa kasuwanninsa na duniya.
342/